Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada
al’adu na muslunci cewa, an tarjama tare da yada sakon jagora kan hajin bana a
kasashe daban-daban.
Bayanin ya ce baya ga tarjama jawabin an kuma saka shi a cikin shafukan yanar gizo gami da jaridu da kafofin yada labarai da daman a kasashen ketare.
Daga cikin kasashen kuwa akwai:
Aljeriya: jaridun Alkhabar, Alshuruq, Akhbar yaum da kuma Alwatan.
Ethiopia: jaridar turanci ta Daily Monitor.
Tunisia: an saka tarjamar jawabin a jaridun Sahwa, da Al-sabah.
Australia: Jaridar mako-mako mai suna Iran.
Turkiya Ankara: a cikin jaridar Aidinlik, sai kuma tashar talabijin ta 14 ta Turkiya.
India: an yada jawabin a tashar WIN da kuma jaridar Sahafat.
Pakistan Kuita: wanna labara ya zoa cikin jaridun Azadi, da Balochestan da kuma Express.
Armenia: a kasar kuma an yada wannan labari a cikin wasu kafofin yada labarai na gidajen talabijin da kuma jaridu na kasar, sai kuma laccoci da aka gudanar a jami’oi wanda masana da suka yi ta gabatarwa da nufin kara sanar da mutane halin da ake ciki.