IQNA

Siyasar Donald Trump Ta Harshen Damo Kan Musulmi

17:49 - September 18, 2016
Lambar Labari: 3480791
Bangaren kasa da kasa, Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyya Republican wasu daga cikin musulmin Amurka sun zarge shi da nuna siyasar harshen damo a kansu.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na Bakersfield cewa, Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyya Republican kuma babban mai udia kasar, ya bude wani katafaren otel a cikin wannan mako, in wasu daga cikin musulmin kasar suka zarge shi da nuna siyasar harshen damo a kansu domin kuwa ya sha furta kalaman batunci da kin jinni gare su, amma kuma daga bisani ya zio ya nuna nuna yana tare da su.

Daya daga cikin wadanda suka shiga cikin tel din tare da kama daki, wanda kuma musulmi ne, ya bayyana cewa ya samu kyauta darduma da kwafin kur’ani a oel din kasantuwar shi musulmi ne.

Ya ce wannan abin mamaki n, domin babu yadda za a yi mutum mai tsananin kiyayya da kyamar musulmi kamar Donald Trump ya yi hakan face da wata manufa da ta daban.

Kamar yadda kuma ya kara da cewa, tun kafin wannan lokacin ya kasance daga cikin mutane wadanda suke kyamar baki ba ma musulmi ba kawai d suke shigowa cikin kasar Amurka, amma daga bisani kiyayyarsa ta fi yawa a kan musulmi, kasantuwar abubuwan ad suke faruwa na ta’addanci inda yake amfani da hakan a matsayin wani makami na siyasa a kan musulmi.

Yanzu dai wannan mataki da Trump ya dauka na raba kur’ani da darduma ga musulmi ya jawo musayar ra’ayoyi a tsakanin Amurka, inda wasu ke ganin cewa ya canja salon siyasarsa ta kin musulmi, yayin da wasu ke ganin cewa yana nan kan bakansa, amma dai tun da ya tafka kure dole ne ya samu wani sabon salo domin yana da bukatar kuri’insu domin ya dare kan kujerar mulki, inda kuma in ya samu mulki su ne farkon wadanda zai fara dandana wa kuda.

3530955


captcha