IQNA

Raba Kwafin Kur’anai A Masallatan Mauritaniya

22:23 - September 21, 2016
Lambar Labari: 3480797
Bangaren kasa da kasa, an raba kwafin kur’anai masu tarin yawa a massalatan birnin Adrar da ke Mauritaniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran gwamnatin Mauritania cewa, majalisar malaman addinin mulsunci ta kasar ce ta dauki nauyin shirin.

Sayyid Muhammad Mahmud Wuld Muhammad Amin shi ne babban darakta na majalisar malaman adini da limaman kasar Mauritaniya, ya bayyana cewa sun fara aiwatar da wanan shiri na alkhairi a garin na Adra, kuma zai ci gaba da yardarm Allah zuwa wasu sauran birane na kasar.

Abdullah Wuld Baha matamakin shugaban majalisar limamai ta kasa ya bayyana cewa, shirin raba kur’anan ya kebanci wasu daga cikin manyan masallatai n a halin yanzu a garin na Adrar, da suka hada da masallacin Atik, Tarik, Ummu Kulsum, Ahlu Tabi, Sunah, Taubah, Tuka, Atar, Aqsa, Aujift dukkaninsu da ke cikin lardin na Adrar.

3531430


captcha