IQNA

Kawancen Wahabiyanci Da Sahyuniya Da Kiyayya Da Shi’a

23:27 - September 27, 2016
Lambar Labari: 3480813
Bangaren kasa da kasa da kasa, wani masani marubuci ya bayyana kawancen wahabiyanci da sahyuniya a matsayin wani sabon makirci na kiyayya da shi’a a duniya.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bratha cewa, Qasem Alajrash wani masani kuma marubuci ne dan kasar Iraki, ya bayyana kawancen wahabiyanci da sahyuniya a matsayin wani sabon makirci na kiyayya da mazhabar shi’a da nfin ganin bayanta.

Marubucin ya ce a cikin ‘yan lokutan nan an ga yadda wahabiyawa suke ta kai komo a haramtacciyar kasar yhudawa, tare da kara karfafa alaka da ke tsakaninsu, tare da fayyace makiyi guda daya wanda suke kallonsa a matsayin makiyi na bai daya, wato jamhuriyar musulunci.

Ya ce hakikanin Magana ba jamhuriyar musulunci ce kawai wannan kawance yake nufi ba, domin kuwa babban abin dayke a matsayin barazana ga wahabiyawa da sahyuniyawa shi ne yaduwar tunani na shi’a duniya, wanda shi ne hakikanin tunani da ya ginu a kan cikakkiyar masaniya ta illar wadannan munanan akidu biyu da suka addabi duniya baki daya.

Akidar sahyuniyanci da wahabiyanci abu biyu ne da suka kama da juna, domin kuwa dukkaninsu sun inu ne akan danne bil adama da zubar da jininsa da yi masa kisan gilla da ta’addanci, abin mamaki kuma dukkanin bangarorin biyu na wahabiyanci da sahyuniyanci suna yin abin da suke yi da sunan addini ne.

Wahabiyawa suna kasha bil adama musulmi da wand aba muuslmi ba da sunan jihadi ko abin da suke kira tafarkin sunna bisa irin akidarsu, yayin da su kuma sahyuniyawa suna kasha bil adama ne da sunan suna bin tafarkin addinin yahudanci, wanda hakan ya hada su a matsayin akidu biyu da suka kama da juna, duk kuwa da cewa suna da alaka da ta hada su, domin kuwa sahyuniyawa suna da hannu wajen kirkiro wahabiyanci a lokacin da suka kafa masarautar iyalan gidan Saud.

Marubucin ya ce dole ne wahabiyawa da sahyuniyawa su yi kiyayya da yan shi’a, domin kuwa sun sani sarai cewa ko da duniya ba ta gane su ba, masana daga cikin shi’a sun san su sarai, musamman kuma jamhuriyar musulunci wadda ta ginu kan kiyayya da sahyuniyanci.

3533109


captcha