IQNA

Gargadi Ga Masu Amfani Da Masallaci Domin Neman Zabe A Morocco

23:37 - October 05, 2016
Lambar Labari: 3480828
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Bunis daya daga cikin malaman addini a kasar Morocco ya yi gargadi dangane da yin amfani da masallaci yakin neman zabe.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nazur city cewa, Muhammad Bunis ya kirayi dukkanin malaman addini musamman ma dai limaman masallatai, da kada su bari a yi amfani da masallatai domin yakin neman zabe.

Malamin ya yi ishara da cewa masallaci wurin ibada ne, yayin da kuma yakin neman zabe Magana ce ta siyasa tsantsa a kasar wadda ba ta da wata alaka da addini, saboda haka bai kamata a fake da addini domin cimma burin a siyasa ba.

Ya kara cewa, abin mamaki ne yadda wasu mutane da ba su da wata alaka da ayyukan masallaci, sai ka gansua suna gyaran masallaci, suna yi masa fyanti da kuma canja kofofi ko tagogi da saka naurar sanya wuri, duk saboda lokacin zabe ya karato, alhali ba su yin hakan a lokutan da ban a zabe ba, kuma hanyar gane hakan ita ce da sun yi hakan kuma sai fitar da butarsu taneman kuri’ar jama’a.

Abin tuni a nn da shi ne wannan shi ne karo na biyu da za a gudanar da zaben yan majalisar dokoki a kasar ta Morocco, tun bayan kafa majalisar da jama’a suka zaba a cikin 2011, kuma za a gudanar da zaben na biyu ne a ranar 7 ga Oktoba na wannan shekara.


captcha