An raba makaloli guda 17 da aka rubuta, wadanda suka kunshi bangarori daban-daban na tunaninsa da ke bayyana yadda yake kallon lamurra ta fskoki da dama a rayuwarsa.
Gungun makalolin da aka mika a wurin sun hada da gabatarwar da Alexendervich shugaban cibiyar ta Anestoti ta tarohi da kuma mohammad Reza Saburi jakadan kasar Iran a Belarus suka rubuta.
Abin tuni a na dai shi ne an fara gudanar da irin wannan taron karawa juna sani ne a lkacin tunawa da rasuwar Imam Khomeini (RA) a ranar 12 ga watan Khordad, wanda kuma kasar ta Belarus na daga cikin wuraren da ake gabatar da irin wanan taro.