Bisa ga wannan rahoto Muhammad Isa ministan kula da ayyukan addini na Algeriya yana cewa, yanayin da ake ciki a kasar na rashin cikar kudaden kasafi ya sanya dole ne a rage wasu daga cikin ayyukan da ake, wanda hakan ya hada har da ginin wasu daga cikin manyan masallatai a lardunan kasar.
A cikin shekara ta 2013 ce dai maia’aikatar kula da harokin addini ta kasar ta fara gudanar da aikin gina manyan masallai a dukkanin manyan biranan kasar, inda kowane masallaci zai dauki masallata akalla dubu 10 a cikinsa.
Ya kara da cewa aikain gina babban masallaci da ake yi a kasar bai samu matsala ba, domin kuwa yanzu ana gab da kammala aikinsa kamar yadda aka tsara, wanda shi ne masallaci na uku mai girma a bayan harami biyu na Makka da masallacin manzo, an kuma fara aikin ginin nasa n tun a cikin shekara ta 2012 ya zuwa yanzu.
Abin tuni a nan dai shi ne, kasar Algeria tana masallatai manya fiye da dubu 15, kuma da dama daga cikin su an gian su ta haynar sadaukarwar al’umma da kudadensu.