IQNA

Taron Yara Na Tunawa Da Kisan Imam Hussain (AS) A Saliyo

22:19 - October 09, 2016
Lambar Labari: 3480840
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taro domin tunawa da kananan yara da suka rasu tare da Imam Hussain (AS) a kasar Saliyo.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin hulda da jama’a na ma’aikatar kula da harkokin al’adu na addini cewa, a ranar Juma’a ta farkon watan moharram, an gudanar da taro domin tunawa da kananan yara da suka rasu tare da Imam Hussain a kasar Saliyo a birane daban-daban na kasar.

Taron ya samu halartar yara da uwayensu mata da dama, inda suka yi alhini kana bin da ya samu uwaye mata da kuma kananan yara a Karbala kamr yadda aya zoa acikin tarihi, musamman Ali Asghar (AS).

3536682

captcha