IQNA

Jami’an Sojin Najeriya Sun Killace Wani Masallaci Da Ake Taron Tasu’a

21:20 - October 12, 2016
Lambar Labari: 3480850
Bangaren kasa da kasa, jami’an sojin gwamnatin najeriya sun killace wani masallaci da ake gudanar da tarukan tasu’a a daren Ashura.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na tashar alalam cewa, jami'an tsaron a birnin Kaduna na tarayyar Nigeria sun yi kawanyya ga wasu yan shia wadanda suke juyayin tasua a cikin wani masallaci a cikin birnin.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta musulmi da ke da mazauni a Landan ta fadawa rresstv mai watsa shirye shiryensa da harshen turanci cewa masallacin yana kan layin Zako kusa da babbar kasuwa na kaduna inda yan shia suke taron na tasu'a.

Kafin haka dai gwamnatin jihar kaduna ta haramta kungiyar yan shia ta Islamic movement in Nigeria IMN wacce ake tsare da jagoranta tun kimanin watanni tara da suka gabata ba tare da gurfanar da shi a gaban kuliya ba.

Kungiyar kare hakkin bil'adaman ta ce ta lura da cewa jami'an tsaron sun hada hatta mata da yara da suka yi kokarin ficewa daga masallacin fita.

Kafin wannan lokacin kami’an tsaron sun kame wasu mutane sha biyar da suke kan hanyarsu ta isa wrin da ake gudanar da wadannan taruka na tasu’a a cikin birnin na Kaduna.

3537369


captcha