Sharif Said matakin na kamfanonin yawon bude-idon na kasar Masar, ya ce; dalilin yin haka shi ne kara kudin fito da kuma na izinin shiga da fice da Saudiyyar ta karawa 'yan kasar waje.
Saudiyyar dai ta kara kudin samun izinin shiga kasar zuwa dalar Amurka dari biyar da talatin da uku.
Masar din dai ta zama kasar farko da ta jingine zirga-zirgar maniyyata zuwa saudiyyar saboda kara kudin samun izinin shiga.
Wannan mataki dai mahukntan na Saudiyya na danganta shi da matakan da suke dauka na kara tado da komadar tattalin arzikin kasar da ke mawuyacin hali.
Sai dai anasu bangaren asana kan harkokin da ke kai da komowa suna ganin cewa, duk da irin mawuyacin halin da tattalin arzikin Saudiyya ke ciki, amma daukar wannan mataki kan masu ziyara daga Masar yana da alaka da siyasa.
A cikin makon da ya gabata ne dai Masar ta kada kuri’a majalisar dinkin duniya da ke mara baya ga daftarin kdirin da maraba da yaki da ta’addanci, lamarin da ya bakanta wa Saudiyya rai matuka, kwanaki biyu bayan haka ta sanar da dakatar da baiwa Masar danyen amn fetur, haka nan kuma ta janye jakadanta.