IQNA

Harin 'Yan Ta'addan Takfiriyya Ya Lakume Rayukan Mutane Fiye Da 31 A Iraki

22:33 - October 15, 2016
Lambar Labari: 3480858
Bangaren kasa da kasa, Sakamakon wani harin ta'addanci da aka kai yau a birnin Bagadaza na kasar Iraki, fiye da fararen hula talatin ne suka rasa rayukansu wasu da dama kuma suka jikkata.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na tashar press TV cewa, 'yan ta'addan wahabiyya takfiriyya sun tayar da wasu bama-bamai a yau a wani wuri da ake gudanar da zaman makokin ashura a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki, inda suka kashe fararen hula fiye da talatin tare da jikkata wasu fiye da hamsin.

Wanann harin dai ya zo ne kwana baya bayan barazanar da ministan harkokin wajen kasar Saudiyyah ya yi wa gwamnatin Iraki ne dangane da shirin da take da shi na fatattakar 'yan ta'addan wahabiyyah takfiriyya na ISIS daga birnin Mausul da suke iko da shi.

Yanzu haka dai sojojin kasar Iraki fiye da dubu dari da arbain ne suke ci gaba da yi wa birnin nan Mausul kawayanya da nufin tsarkakae shi daga 'yan ta'addan wahabiyyah takfiriyya na ISIS, lamarin da ya daga hankulan gwamnatocin da ke daukar nauyinsu, musamman Amurka, Saudiyya da kuma turkiya da kawayensu.

3537897


captcha