Kasashe da dama sun nuan rashin gamsuwarsu da abin da Saudiyyah ta yi, daga ciki har da kasashen da suke binta kasashen da suka nuna kurafi suna da dama da suka hada da Jordan, Masar, Morocco, kamar yadda ita ma Turkiya ta ki amincewa da hakan.
Wanann mataki ya sanya kamfanonin zirga-zirga na jiragen sama a kasar Masar sanar da dakatar da duk wani aikin ziyara zuwa kasar saudiyya, sakamakon daukar wannan mataki da suke kallonsa na takura jama’a ne.
A kasar Afirka ta kudu ma musulmi sun nuna fushi da damuwa kan wannan lamari, inda suke ganin cewa hakika daukar wannan mataki yana da alaka da wasu sabbin manufofi na mahukuntan kasar Saudiyya na huce haushinsu kan musulmi masu ziyara sakamakon matsalolin tattalin arzikin da suka jefa kansu.
Yusuf Abramiji shi ne shugaban majalisar musulmi a kasar Afirka ta kudu ya bayyana cewa, ko alama bas u amince da wannan mataki da mahukuntan Saudiyya suke shirin dauka ba.
Ya kara da cewa yanzu haka dai sun mika wasu wasiku zuwa ga ofishin jakadancin kasar Saudiyya da ke kasar, kuma suna jiran jawabi duk da cewa sun aike da wasiku da dama amma har yanzu ofishin na Saudiyya ya ki ba su jawabi ba.
Abramiji ya ce sarkin Saudiyya ba zai iya sauke haushinsa a kan musulmi ba, domin kuwa don kasarsa na fama da matsalar tattain arziki hakan ba dalili ba ne na tsawwala ma sauran musulmin duniya.