IQNA

An Rufe Masallatan Karkuk

23:54 - October 21, 2016
Lambar Labari: 3480872
Bangaren kasa da kasa, sakamakon harin da aka kai yau a Karkuk malaman sun umarci a rufe dukkanin masallatansu.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, jaridar quds Alrabi ta bayar da rahoton cewa, malaman sunna na birnin karkuk sun rufe masallatansu.

Bayanin y ace malaman sun fitar da wannan sanarwa nea yau, sakamakon hare-haren ta’addanci da da aka kai agarin, inda suka ce jami’an tsaro bas u iya bayar da kariya ga muhimman wurare na gwamnati balatana masallatai.

A yau yan ta’adda suka kaddamar da hari kan wata tashar samar da wutar lantarki, inda suka kasha mutane da dama da suka hada har da Iraniyawa hudu.

Wannan tashar wutar lantarki tana nisan kilo mita 45 ne daga birnin karkuk, inda hudu daga cikin wadanda suka rasu injiniyoyi ne kasar da suke aikia awurin.

3539509


captcha