
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya
habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran stripes ya habarta
cewa, jami'an tsaron sun kame mutumin ne mai suna Mark Lusion Figin dan shekaru
41 bayan da ya rika shelanta cewa yana da shirin kai hari a kan babbar cibiyar
musulmi da kuma masallansua a cikin yankin Califirnia ta kudu, inda suka
kai same a gidansa.
Hores Frank babban kwamishin nan 'yan sanda na
Los Angeles ya sheda ma manema labarai cewa, jami'ansa sun kai samame a gidan
Figin sun kuma samu tarin makamai da suka hada da bindigogi gami da wasu
sanadari masu hadari, wanda hakan yasa a ka kame shi, kuma yanzu haka ana bincike
kan lamarinsa.
3540914