Ahmad Tayyib babban malamin Azhar tare da Justin Wellby babban masanikuma shugaban majalisar manyan malaman majmi’ar Angalican, inda dkkanin bangarorin biyu suke tafe da tawaga da ta kunshi masana.
Babbar manufar gudanar da wannan zama dai ita ce kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai na kiristanci da muslunci, da kuma yadda mabiya wadannan manyan addinai za su ci gaba da zama lafiya da juna, tare da kin amincewqa da duk wani tsatsauran ra’ayi d zai kawo kiyaya a tsakaninsu.
An fara gudanar da wannan taro ne dai tuna cikin shekara ta 2015 a birnin Florance na kasar Italiya, daga nan kuma sai a birnin Paris na kasar Faransa, an kuma gudanar da zama na uku a bin Geneva fadar mulkin Switzerland.