IQNA

23:45 - November 02, 2016
Lambar Labari: 3480901
Bngaren kasa da kasa, an gano wani kwafin kur’ani mai tsarki a cikin lardin Buhaira na kasar Masar wanda aka rubuta da hannu a masallacin Sidi Atiyyah Abu Rish.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misri Alyaum cewa, Muhammad Sha’alan babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini ta yankin Buhaira ya bayyana cewa wannan lamari ne mai matukar muhimmanci.

Ya kara da cewa wannan kwafin kur’ani mai tsarki da aka samu, yana komawa ne zuwa ga daruruwan shekaru da suka gabata, weanda hakan kuma yake nuni da matsayin wannan littafi mai tsarki.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, wannan littafi mai tsarki alama ce ta ilimi da kuma wani abu mai matukar kima na tarihi a kasar Masar, wanda baikebantu da wani mutum ba shi kadai, lamari ne na al’ummar Masar baki daya.

Shi ma anasa bangaren ministan kula da harkokin addini na kasar Mukhtar Jma’a ya bayyana cewa, za a dauki wannan kwafin kur’ani tare da adana shia wani wuri na muasamman.

3542751


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، Buhaira ، masar ، addini ، ishara
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: