IQNA

19:48 - November 08, 2016
Lambar Labari: 3480919
Bangaren kasa da kasa, sansanonin da ake kafawa domin gudanar da ayyuka da suka shafi kur'ani a kan hanyar masu ziyarar arab'in sun fara aiki.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hubbaren Alawi mai tsarki cewa, shirin kur'ani a kan hanyoyin masu ziyara musamman daga Basara ya fara gudana.

Wannan shirin yana gudana a kowace shekara a duk lokacin da ake gudanar da tattakin ziyarar Imam Hussain (AS) inda mutane sukan gudanar da karatun kur'ani tare da koyar da tajwidi da hukuncin karatun ga wadanda suke da rauni.

Shirin dai yana samun karbuwa daga masu ziyara, kamar yadda malamai sukan bayar da gudunmawa wajen ganin sun taimaka ma mutane domin tabbatar da cewa shirin ya yi nasara.

Amir Ka'abi shi ne mai jagorantar wannan shiri, ya bayyana cewa hakika sun jima da kammala shirinsu, kuma tuni aka fara kafa sansanonin kur'ani ga masu tattakin arba'in a kan hanyoyin isa birnin karbala mai alfarma, inda a halin yanzu an kafa sansani kimanin 21 a kan hanyar Basara zuwa Karbala.

Ya kara da cewa, baya ga karatun kur'ani da koyar da hukuncin karatunsa da kuma bayanan ayoyinsa da malamai ke yi a wadannan sansanoni, ana yin tuanatwar ta addini da wa'azi ga jama'a kan lamurra da suka shafi ziyarar da sauran batutuwa na zamantakewa.

3544280


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: