IQNA

23:07 - November 11, 2016
Lambar Labari: 3480930
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta wa dubban mutane daga Gaza halartar sallar juma’a a birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta palastinu ta sanar da cewa, gwamnatin yahudawa ta sanar da cewa daga palastinawa ba za su sake fita da Gaza zuwa birnin Auds domin halartar sallar Juma’a ba.

Wannan mataki dai ya zo bayan hana palastinawa da dama da suke yankunan gabar yamma da kogin Jordan halartar sallar Juma’a a birnin Quds da haramtaciyar kasar Isra’ila ta yi a lokutan baya, saboda abin da ta kira dalilai na tsaro.

Mutane da dama daga yankin zirin Gaza, sukan halarci sallar Juma’a a masallacin Quds a kowane mako, ama daga yau yahudawa sun haramta musu hakan.

3545018


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، haramta ، Gaza ، Quds ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: