Ya ce yana yaro karami da ya saka shi hanyar karatu tun yana karami wanda a halin yanzu ya kai shekaru goma sha uku, kuma ya riga ya koyi dukkanin abin da ake bukata, saboda kwalwar yaro ta fi saurin daukar abu fiye da kwalwar babba.
Dangane da muhimmancin da ke tatatre da motsa jiki da kuma yadda yake taimaka ma masu karatun kur'ani ya bayyana cewa, a lokaci guda kuma yan ada kyau a rika barin yara suna yin wasa da motsa jikinsu, domin shi ma zai taimaka masa.
Malamin ya ce dansa wanda a halin yanzu ake lissafa shia cikin mkakaranta ya tabbatar masa da cewa, wasan kwallo da yake ya taimaka masa matuka wajen samun nishadi da kuma yin harda da karatu cikin sauki.