IQNA

20:33 - November 18, 2016
Lambar Labari: 3480950
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron gwamnatin Najeriya sun kai farmaki kan wata Husainiyar mabiya mazhabar shi'a tare da rusheta baki daya.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shadin shafaqna cewa, jami'an tsaroa cikin kayan sarki sun kaddamar da farmaki kan wata cibiyar Husainiya da mabiya mazhabar shi'a ke gabatar da tarukansu an addini a garin Saminaka da ke cikin jahar Kaduna.

Jami'an tsaron sun zo tare da ma'aikatan rusau, wadanda suka markade ginin baki daya, kafin daga bisani kuma mutanen gari suka shiga satar kayan da ke wurin, da suka hada da littafai na addini kur'anai da sauransu.

Wannan yazo kwanaki biyu da kai wani farmakin a garin kano kan masu tattaki da ke nufin zuwa Zaria domin raya ranar arbaeen na Imam hussain (AS) da suka saba gudanarwa a kowace shekara, inda jami'an yan sanda suka bude wutar bindiga a kansu tare da kasha adadi mai yawa daga cikinsu.

An dai gudanar da janazar mutane takwas da ke hannun 'yan shi'an na harkar islamiyya, yayin rahotanni ke cewa jami'an tsaron sun kasha mutane kimanin dari, kuma sun bizne su a wasu wurare da ba a sani bayan da suka kasha su daga inda suka kasha su.

Wata yarinya kara mai suna Zainab ita ce mafi karancin shekaru daga cikin wadanda 'yan sanda suka kashe a wurin.

3546908


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، Najeriya ، Kaduna ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: