IQNA

23:26 - November 19, 2016
Lambar Labari: 3480955
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron gwamnatin Najeriya nba ci gaba da kara tsananta hare-harensu a kan mabiya mazhabar shi’a na kasar.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic Movement cewa, jagororin harkar muslucni a Najeriya sun sanar da cewa, jami’an gwamnatin kasar na ci gaba da rusa makarantu da asibitoci gami da cibiyoyin addini na Husainiya na mabiya mazhabar shi’a a garuruwan Zaria da kuma Saminaka.

Wannan mataki dai ya zo ne kamar yadda ta kasance a lokutan baya, ba tare da wata sanarwa ko bayar da notis, jami’an tsaro sun zo da manyan motoci suna rusa wurare da nike dukkanin kaddarorin da ke ciki.

Koa cikin makon da ya gabata jami’an tsaron gwamnatin Najeriya sun afka kan mas tattakin arbaeena cikin jahar Kano, inda suka kasha mutane kimanin 100 da ska hada da mata da kanan yara, bisa hujjar cewa suna dauke da makamai, da suka hada da wukake da danko.

A shekarar da ta gabata ce dai jami’an sojin Najeriya suka kai hari a kan mabiya mazhabar shi’a a Zaria’ tare da kashe adadi mai yawa daga cikinsu, bisa hujjar cewa sun tare wa babban hafsan sojin kasar hanya, inda gwamnatin Kaduna ta tababtar da cewa an bizne kimanin 350 daga cikinsu a rami guda, yayin mabiya harkar muslunci suka ce sojojin Najeriya sun kasha ‘yan uwansu fiye da dubu daya.

3547210


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، Najeriya ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: