IQNA

23:52 - November 23, 2016
Lambar Labari: 3480966
Bangaren kasa da kasa, an bayar da gurbin karatu na addini ga mabiya mazhabar iyalan gidan manzo yan Najeriya a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NUN cewa, sheikh Badamasi Ya’akub dan uawan sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran mabiyar mazhabar shi’a a najeriya tare da wasu mutane kimanin 60 sun gana da Sheikh Mahdi karbala’I wakilin Ayatollah Sistani a birnin karbala mai alfarma.

Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin ganawar tasu sun tattauna muhimamncin da ke tattare da neman ilimi, wanda kuma kuma ko shakka babu wasu da dama daga mutanen Najeriya suna da shawar su je su karatu na addini a kasar ta Iraki, a kan haka aka bayar da guraben karatu ga mutane goma sha daya daga cikin mabiya harkar musulunci.

Hka nan kuma a nasu bangaren malamai da dama akasar ta Iraki sun nuna farin cikinsu danagne da yadda yan Najeriya da dama suka samun damar zuwa tattakin arbaeen na Imam Hussain a wannan shekara da wasu shekaru da suka gabata.

Kamar yadda suka yi fatan ganin mahukuntan Najeriya sun saki jagoran harkar muslunci da suke tsare da shi a halin yanzu domin samun damar yi masa magani.

Su ma a nasu mabiya harkar musulunci yi godiya matuka dangane da irin karamcin da aka nuna msuu a wannan trao mai albarka daga bangaren al’ummar kasar Iraki.

3548302


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: