IQNA

23:53 - November 23, 2016
Lambar Labari: 3480967
Bangaren kasa da kasa, wata mata musulma 'yar kasar Azarbaijan, ta rubuta cikakken kur'ani mai tsarki da hannunta a kan kyallayen alhariri.
Kmfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto dag shafin yada labarai na jaridar daily Sabah cewa, Wata mata musulma mai suna Tunzal Muhammad Zadah 'yar kasar Azarbaijan yar shekaru 33 da haihuwa,ta rubuta cikakken kur'ani mai tsarki da hannunta a kan kyallayen alhariri, tare da yin amfani da tawada da aka hada ta da ruwan zinari da azurfa.

Bayanin ya ci gaba da cewa yana daga cikin ayyuka da aka gudanar masu daukar hankali matuka da suka danganci kur’ania cikin tarihi, kuma wannan kwafin kur’ani ya shiga cikin tarihi.

Wannan mata dai ta dauki shekaru kimani uku a jere tana gudanar da wannan aiki mai babbar kima, wanda kuma cikon ikon Allah ta samu nasarar kammala aikin a cikin wannan shekara.

Da dama daga cikin masana sun nuna mamakinsu matuka dangane da yadda wannan mata ta gudsanar da wannan gagarumin aiki a cikin kankanin lokaci.

354816


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، Azarbaijan ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: