IQNA

Jagoran Juyi:
21:29 - November 26, 2016
Lambar Labari: 3480974
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin islama na Iran a lokacin da yake ganawa da dakarun sa kai na kasar ya bayyana cewa, idan har aka aiwatar da sabunta takunkumi a kan Iran na tsawon shekaru 10 to hakan ya yi hannun riga da yarjejeniyar nukiliya.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan dakarun sa kai na Iran, inda ya bayyana dakarun sa kai din a matsayin wasu "dakaru na juyin juya hali' kana kuma "alama dake tabbatar da tsarin demokradiyya na addini' wanda ya dogara bisa basira. Haka nan kuma yayin da yake jaddda wajibcin gudanar da tsare-tsare masu kyau don kara karfafa kasantuwar dakarun basij din a fagage daban na al'umma, Jagoran ya bayyana cewar: Ruhin Basiji shi ne jin cewa a koda yaushe Allah yana tare da mutum kana da kuma rashin yanke kauna da mutuwar gwiwa. A saboda haka ne muke gaya wa mutanen da suke fuskantar matsalar raunin zuciya da kuma tsoron makiya da kuma jin cewa lalle mu ba za mu iya ba cewa ta hanyar dogaro da karfi na Ubangiji da kuma yarda da karfin da ake da shi, za a iya magance dukkanin matsalolin da ake fuskanta sannan kuma babu wani karfin da za a ji tsoronsa.

A farkon jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya bayyana gagarumin jerin gwanon Arba'in da aka yi a matsayin wani lamari da ke cike da tarihi kana kuma abin da ke nuni da karfin Ubangiji yana mai cewa: Tabbas ana iya iya ganin karfi na Ubangiji cikin irin wadannan abubuwa masu tarihi irin su wannan jerin gwano na Arba'in ko kuma lamurra irin su kame ofishin jakadancin Amurka da aka yi a Tehran ko kuma gagarumin yunkurin 9 ga watan Dey na shekarar 1388 (2009) da kuma i'itikafin da ake shiga wadanda ba wai kiran mutane aka yi ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran a matsayin irin wadannan abubuwa da ake ganin taimakon Ubangiji cikinsu inda ya ce: Lalle a fili ake irin ganin wannan taimako na Ubangiji cikin fitowar mutane da kuma yadda aka kafa juyin juya halin Musulunci, kamar yadda marigayi Imam Khumaini yake fadi ne cewa lalle ya kasance yana ganin karfin Ubangiji cikin wannan yunkuri na al'umma tsawon lokacin juyin juya halin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin gagarumin jerin gwano da tattakin miliyoyin mutane a ranar Arba'in na Imam Husain (a.s) a matsayin wani lamari ne da ke nuni da kaunar da take cike da basira. Jagoran ya ci gaba da cewa: Muna yi wa masu ziyarar da suka sami damar aiwatar da wannan babban aiki barka da zuwa da kuma rokon Allah Ya karba musu, kamar yadda kuma muke mika godiyarmu ga al'ummar Iraki saboda irin wannan wannan karbar bakunci mai kyau da suka yi musu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar wajibi ne mutane su zama masu godiya ga wannan ni'ima ta Arba'in da kuma kiyaye irin abubuwan da ake samu a cikinta.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wasu mutane suna ta kokari wajen kawarwa ko kuma gurbata wannan lamari mai cike da haske na Arba'in, wanda kuma ba za su sami nasarar hakan ba. Ko shakka babu wannan babbar ni'ima za ta zamanto abar girma da daukaka ga al'ummomin Iran da Iraki.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi karin haske dangane da batutuwan da suka shafi Iran da gwamnatin Amurka ma'abociyar girman kai inda ya ce: Mu dai a halin yanzu ba za mu yi hukunci dangane da sabuwar gwamnatin da za ta kama aiki a Amurka ba, to amma gwamnati mai ci yanzu ma dangane da batun yarjejeniyar nukiliya ba ta yi aiki da nauyin dake wuyanta kamar yadda aka cimma ba, sannan kuma kamar yadda a farko jami'anmu suka ce za ta yi aiki da shi ba.

Haka nan yayin da yake magana kan sake sabunta dokar takunkumin shekaru 10 da aka sanya wa Iran da majalisar Amurka ta yi, Jagoran ya bayyana cewar: Matukar dai aka aiwatar da wannan takunkumin, to kuwa hakan karya yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma ne. Ya kamata su san cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ko shakka babu za ta mayar da martani.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Bai kamata yarjejejeniyar nukiliyan ta zamanto wani makami na yin matsayin lamba wa al'ummar Iran ba.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da maganganun jami'an gwamnatin Iran da kuma jami'an da suka jagoranci tattaunawar nukiliyan na cewa manufar tattaunawar ita ce dauke takunkumi da matsin lambar da ake yi wa al'ummar Iran, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Gwamnatin Amurka ba ya ga wadannan alkawurra da ba ta cika da kuma nauyin da ke kanta dangane da yarjejeniyar da ba ta cika ba ko kuma ba ta yi abin da ya dace ba - wanda kuma a fili ma jami'an da ke kula da yarjejeniyar sun fadi hakan - a halin yanzu kuma sun mayar da yarjejeniyar ta zamanto wata hanya ta matsin lamba wa Iran.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar dogaro da karfi na Ubangiji da kuma yarda da irin karfi na kasantuwar mutane, lalle ba ta jin tsoron duk wani karfi a duniyar nan.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Idan har wani, bisa koyi da irin rauni na Bani Isra'ila ya fadi cewa "Lalle mu ba za mu iya ba", sannan kuma ya kasance yana jin tsoron makiya, to mu kuwa za mu yi koyi da Annabi Musa (a.s) wajen ba su amsar cewa lalle ba haka lamarin yake ba don kuwa Allah Madaukakin Sarki Yana tare da mu, kuma lalle zai shiryar da mu.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci sai da Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar ta Iran da kuma Laftanar Janar Muhammad Ridha Naqdi shugaban hukumar dakarun Basij din na Iran suka gabatar da jawabansu da kuma bayyana irin shirin da dakarun na Basij suke da shi na kare kasar Iran daga duk wata barazana ta makiya.

3548197


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: