Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron kasar Iraki sun sanar da hana jama'a kai komo a cikin garin Samirra saboda dalilai na tsaro, da kuma kare rayukan jama'a daga hare-haren 'yan ta'adda.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya
habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillanicn labaran Shafaq News daga Iraki
ya bayar da rahoton cewa, wasu bayanan sirri da jami'an tsaro suka samu sun
tabbata musu da cewa wasu gungun 'yan ta'addan takfiriyya sun shiga birnin
Samirra a yau, kuma dukkaninsu suna daure da jigidar bama-bamai a jikinsu.
Wannan ya sanya jami'an tsaron bayar da sanar
ga al'ummar garin kan cewa kowa ya zauna gida, kuma ana cikin gudanar da
bincike kan wani lamari da ya danganci tsaro.
A kwanakin baya 'yan ta'addan takfiriyyah sun
tayar da bama-bamai a kusa da birnin na Samirra, tare da kashe adadi mai yawa
na masu ziyarar wuraren ziyara da ke birnin.
3549641