IQNA

Palastinawa 50 Sun Samu Raunuka A Bata Kashi Da Sojojin Sahyuniya

20:26 - December 01, 2016
Lambar Labari: 3480992
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wani artabu da aka yi tsakanin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma matasan Palastinawa a yankin Abu Dis da ke Gabshin Quds Palastinawa da dama sun jikkata.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastinu cewa, matasan palastinawa da dama sun samu raunuka sakamakon yin amfani da karfi da sojojin Isra’ila suka yi a kansu.

Matasan wadanda akasarinsu daliban jami’a ne sun fito a kusa da jami’a suna nuna rashin amincewarsu da zaluncin da suke fuskanta daga gwamnatin yahdawan sahyuniya da ta mamaye musu yankuna.

Sojojin mamayar sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da ke dauke da sanadarai masu guba, da kuma harsasan roba wajen tarwatsa matasan, inda suka jikkata wasu da dama daga cikinsu.

Cibiyar Hilal Ahmar ta Palastine ta ce 10 daga cikin wadanda suka samu raunka an harbe su ne da harsasan bindiga na roba, yayin da wasu 39 kuma lumfashinsu yana daukewa ne sakamakon shaker iskar gas mai guna da sojojin yahudawan suka yi amfani da shi a kansu.

Tun daga lokacin da palastinawa suka fara intifadar Aqsa a cikin watan Oktoban shekara ta 2015 ya zwa yanzu fiye da palastinawa 260 ne uska yi shahada, wasu daruruwa kuma suka samu munanan raunuka.

3550141


captcha