Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na ma’a cewa, yan sandan haramtacciyar kasar Isra’ila sun kara yawan sa’oin da yahudawan sahyuniya yan share wuri zauna suke shiga masallacin aqsa daga karfe bakwai da rabi na safe har zuwa sha daya na rana.
Sheikh Azalim Khattab babban daraktan cibiyar kula da harkokin addini ta Palastinu ya bayyana cewa, wannan mataki da yahudawan sahyuniya suka dauka ya kara tabbatar wa al’ummar musulmi cewa a hankali a hankali yahuadawa za su yi duk abin da za su iya domin tabbatar da sun kwace wannan masallaci daga hannun musulmi.
Ya ci gaba da cewa za su kalubalanci wannan mataki da dukaknin karfinsu, ta hanyar kin amincewa da hakan a hukumance da kuma bin hanyar wayar da kan jama’a da suki amincewa da hakan domin tabatar da cewa an kare hakokinsu.
Khattab ya kara da cewa, wannan mataki da jami’an tsaron yahudawa suka dauka ba wani abu ba ne illa tsokana, domin sun yi abubuwa da dama da za su tsokani al’ummar palastinu domin samu hujjar afka musu, kuma suna ganin wannan ita ce hanya mafi sauki gare su domin fusata palastinawa.