Kamfanin dillancin labaran kr’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadsarwa na yanar gizo na jaridar Qus Al-arabi cewa, Abubakar Kan’an babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini a lardin Nainawa ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan Daesh sun rusa masallatai 104 a cikin wannan guduma a cikin shekaru.
Ya ce tun daga shekara ta 2014 da ‘yan ta’addan suka kwace iko da wannan lardi, sun rusa masallatai 37 wadanda suke da muhimamnci ta fuskar tarihi a kasar Iraki, sakamakon wadannan masallatai suna kusa da kabrukan wasu salihan bayi, da suka hada har da kabrukan annabawa, inda suke rusa masallatan da kuma kabrukan da ke wurin.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, wasu daga cikin masallatan an rusa su ne a baya-bayan nan, sakamakon artabun da ake yi da ‘yan ta’addan, inda suke fakewa da masallatai tare da mayar da su tungarsu, kamar yadda kuma sukan saka nakiyoyi a cikin masallatai a lokacin da suka bar wurin, da nufin kasha sojojin Iraki.
Tun kimanin shekaru biyu da suka gabata ne yan ta’addan Daesh suka shiga arewacin Iraki tare da taimakon wasu daga cikin kasashen larabawa da suke makwaftaka da Iraki, inda ya zuwa yanzu sun kasha dubban fararen hula awadannan yankuna, akasarinsu kuma ‘yan sunna ne.