IQNA

Trump Na Shirin Mayar Da Ofishin Jakadancin Amurka A Isra’ila Zuwa Quds

23:45 - December 13, 2016
Lambar Labari: 3481032
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump na da shirin dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, Clean Canavy bababn mai baiwa Trump shawara kan harkoki na kasa da kasa, ya bayyana cewa kamar yadda Trump ya yi alkawalia lokacin yakin neman zabe, kan cewa zai mayar da ofishin jakadancin Amrka a Isra’ila zuwa Quds, yana nan kan bakansa.

Ya ce hakai wannan yan adaga cikin muhimamn ayyukan da Trump zai fara a iwatar idan ya shiga fadar white house, kuma ya yi imanin cewa yahudawan Isra’ila za su farin ciki matuka da yin hakan.

Donald Trump na da nufin gabatar da wannan Magana a gaban majlaisar dokokin kasar idan aka rantsar da shi, kuma ga dukkanin alamau majalisar dokokin Amurka za ta amince da hakan, wanda hakan zai tababtar wa duniya duniya Amukra ta amince a hukumance da mamayar birnin Quds da Isra’ila ke yi.

Wannan mataki zai zama shi ne irinsa nafarko, domin kwa hatta sauran kasashen turai masu kare Isra’ila ido rufe, sun ki amincewa da su mayar da ofisoshin jakadancinsu zuwa Quds.

3553587


captcha