IQNA

Binciken Ayar Kur’ani sau Dubu 2 Bayan Harin Coci A Masar

23:48 - December 13, 2016
Lambar Labari: 3481033
Bangaren kasa da kasa, bayan harin ta’addancin da aka kai kan wata coci a birnin Alkahira na kasar Masar, an ta nema aya ta 32 a cikin surat Ma’idah wadda ta haramta kisan ran dan adam.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yaum Sabi cewa, jim kadan bayan kai harin cocin birnin Alkahira, an ta yin nema a shafin google kan aya ta 32 a cikin surat maidah, wadda ke cewa; Duk wanda ya kashe wani rai ba da hakkin wani ran ba ko kuma ya yi barna a bayan kasa kamar ya kashe mutane ne baki daya, wanda ya raya ta kamar ya raya mutane ne baki daya.

Haka nan jim kadan bayan kai harin, an yi bincike a shafin yanar gizo kan kalmomin jana’aizar shahidan cocon Abbasiyyah, da kuma kalamr shahidan Pitrasiya, an bincike kan kalma ta farko sau 5000, kalma ta biyu kuma sai kimanin 2000.

Baya ga binciken Kalmar harin ta’addancin cocin Abbasiyya wanda ya kais au 5000 a google, haka nan kuma Kalmar hare-haren yau, an bincike a kanta har sau kimanin 5000 shi a shafin na bincike na yanar gizo jim kadan bayan kai harin.

3553508


captcha