IQNA

An Kirayi Cibiyar Azhar Da Ta Taka Rawa Wajen Hada Kan Al'ummar Musulmi

16:25 - December 17, 2016
Lambar Labari: 3481043
Bangaren kasa da kasa, An bukaci cibiyar Azahar da ta taka gagarumar rawa wajen ta hada kan cibiyoyin musulmi a dukkanin fadin duniya da suke da mahanga daban-daban kan batutuwa na addini.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Sheikh Badruddini Hassun babban malami maia bayar da fatawa na kasar Syria ya yi wannan kira a taron makon hadin kai da yake gudana a birnin Tehran na kasar Iran, wanda yake samun halartar manyan malamai da masana daga kasashen duniya daban-daban.

Sheikh Hassun ya ce bisa la'akari da halin da al'ummar musulmi ta samu kanta a cikin a yanzu, ya zama wajibi a kan dukkanin manyan cibiyoyin addini masu karfin fada a ji a duniya da su taka gagarumar rawa wajen fadakarwa da za ta hada kan musulmi tare da dinke baraka a tsakaninsu.

Ya ce Cibiyar Azhar a matsayinta na bababr cibiyar 'yan sunna ta duniya, tana gagaruwar gudunmawa da za ta iya bayarwa a wannan fage, musamman idan aka yi la'akari da irin gudunmawar da bangaren Iran ke bayarwa daga nata bangaren.

Tun kimanin kwanaki uku da suka gabata ne dai aka fara gudanar da zaman taron na makon hadin kai, inda ake duba batutuwa da ya kamata a mayar da hankali a kansu wajen hada kan musulmi, da kuma fuskantar abin da ke gabansu maimakon tsayawa a kullum suna sukar juna sabon banbancin fahimta.

Kamar yadda kuma ake tatatuna yadda za a fuskanci mummuanr akidar nan da ta kunno kai a cikin al'ummar msuulmi ta takfiriyyah, wadda kan yi sanadiyyar shigar matasan msuulmi cikin kungiyoyin ta'addanci da sunan addini.

3554206


captcha