IQNA

Iran Za Ta Dauki bakuncin Wani Taro Kan Tattaunawar Addinai tare Da Austria

22:53 - December 21, 2016
Lambar Labari: 3481055
Bangaren kasa da kasa, jamhuriyar muslunci ta Iran za ta dauki nauyin gudanar da wani zaman taro danagane kara kusanto da fahimta a tsakanin addinai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labarai na ma'akatar al'adu cewa, Muhammad Mahdi Taskhiri shi ne zai jagoranci wannan zaman taro, wanda zai kunshi bangarorin malamai na Iran da kuma na majami'ar kiristoci ta Austria.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zama a za a gudanar da shi ne a cikin wannan shekara mai kamawa, wanda kuma zai tabo batutuwa masu matukar muhimamnci ga dukaknin bangarori na musulmi da kiristoci.

Daga cikin abubuwan da za atattauna a kansu akwai batun yadda za a hada karfi da karfe domin kara fahimta da samar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinaia dukkanin bangarori na duniya.

Kamar yadda kuma za a yi dubi kan yadda wasu suke kokarin nuwa kiristoci cewa musulunci addinin ta'addanci, da kuma yadda za a kawo karshen wannan mummunar fahimta, wadda take sanya wasu kyamar musulmi a kasashen turai musamman.

Kasar Austria dai na daga cikin kasashen da suke taka gagarumar rawa wajen ganin an samu zaman lafiya aduniya, kamar yadda majami'oin mabiya addinin kirista su ma suke yin irin wannan kokari.

3555650


captcha