Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga wam cewa, Ministocin harkokin Wajen na kungiyar tarayyar turai da larabawa suna kin amincewa da gina matsugunan yahudawa yan share wuri zauna.
Tashar telbijin din Press tv ta ambato majiyar kungiyar hadin kan kasashen larabwa su ka yi taron hadin guiwa da tarayyar turai a birnin alqahira, na Masar, suna bayyana matsugunan yahudawa 'yan share wuri zauna da haramtacciyar kasar ta ke ginawa da cewa sun sabawa doka.
Bugu da kari, kungiyoyin sun bayyana amfani da karfi da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta ke yi domin tilastawa palasdinawa matsuguninsu da cewa yana cin karo da dokokin kasa da kasa.