Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habrta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nur Press cewa, a cikin bayanin da ma’aikatar kula da harkokin addini ta Morocco ta fitar, ta bayyana cewa a cikin wannan shekara ta 2016 an gina masallatai 195 a kasar baki daya.
Wannan aiki wanda bangaren kula da harkokin masallatai na kasar Morocco a ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ke gudanarwa, ya hada har da gyaran wasu daga cikin msallatai da suka samu matsala.
Wannan aiki baki daya ya lakume tsabar kudade da suka kai Dirham miliyan 755 da dubu 235, kamar yadda aikin gyaran masallatan ya lakume dirhami miliyan 90, sai kuma sauran aikin ginin masallatan ya cinye sauran kudin da suka kai dirhami miliyan 665, da dubu 235 a jimlace.