A cikin watannin da suka gabata ne dai masarautat Bahrain ta sanar da cewa ta janye izinin zama dan kasa daga sheikh Isa Kasim, saboda goyon bayan masu adawa da gwamanti da masarautar ta ce yana yi.
Tun bayan da masarautar Bahrain ta sanar da janye izinin zama dan kasa daga kan malamin kimanin makonni 23 da suka gabata, ta hana gudanar da sallar Juma'a a yankin na Diraz baki daya, musamman a masallacin Imam Sadiq (AS) da shehin malamin ke bayar da sallar Juma'a.
Ko a cikin wannan makon daruruwan jami'an 'yan sandan masarautar Bahrain tare da rakiyar motoci masu sulke sun kai farmaki a unguwar Diraz da nufin kama sheikh Isa Kasim, amma dubban jama'a da ke wurin sun tare gabansu, tare da hana su isa zuwa gidan, lamarin da ya tialsta 'yan sanda ficewa daga yankin babu shiri.