IQNA

An Yi Umarnin Kwace Wani Littafin Mai Aibanta Annabawa A Aljeriya

22:43 - December 29, 2016
Lambar Labari: 3481081
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Aljeriya ta bayar da umarnin kwace wani lttafin addini da aka buga domin yara 'yan makaranta.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Albilad ta kasar Aljeriya, ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar ya yi umarmi da akwace kwafin wani littafi da aka rubuta kan kissoshin annabawa, bayan da aka gano cewa akwai maganganu da suka sabawa koyarwar addini a kan tarihin annabawa.

Littafin wanda Taufiq Musa ya rubuta, an yi shi ne domin koyar da kananna yara tarihin annabawa, a makarantu, amma bayan gudanar da bincike kan littafin da abin ya kunsa, ma'aikatar addini ta kasar ta ce akwai cin zarafiga manzon Allah a cikin wasu kissoshin.

Yan haka dai an raba dubban kwafi-kwafi na wannan littafi a makarantun islamiyya da dama na kasar gami da wasu cibiyoyin ilimi.

Ministan ya umarci limamai a dukkanin fadin kasar da yi sanarwa domin a hada dukkanin kwafin littafin a tabbatar da an fitar da shi daga hannun jama'a.

3557492


captcha