Babbar cibiyar kula da masallacin quds ta bayyana cewa, wannan mataki yana zuwa da nufin tsokanar dukkanin al'ummar musulmi na duniya, domin wannan masallaci wanda yake shi ne alkibla ta farko ta musulmi, mallakin dukkanin musulmi ne na duniya.
Cibiyar ta ce ya kamata yahuwan sahyuniya su kwana da sanin cewa abin da suke yi yana da matukar hadari gare su, domin kuwa musulmi ba za su sanya ido a rusa masallacin aqsa ba.
Tun kafin wannan lokacin jami'an haramtacciyar kasar Isra'ila sun sanar a hukumance cewa za a kammala aikin gina wadanan ramuka a karkashin masalalcin, domin hada wadil hulwa da kuma kofar magariba, inda yahudawa za su rika kai komo a karkahsin masalalcin da sunan ibada.
A cikin wannan makon ne yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi za su shiga masalalcin aqsa domin gudaar da bukukuwan idin yahudawa na Hanuka, inda za su ci abinci da raye-raye da shaye-shaye.
Tuni dai gwamnatin Isra'ila ta dauki matakan bayar da kariya ga wannan biki da yhudawan za su a cikin masalalcin quds mai alfarma.