IQNA

Wata Likita A Masar na Shirin Fitar Da Littafin Ilimin Magunguna Daga Kur'ani

21:46 - January 02, 2017
Lambar Labari: 3481094
Bangaren kasa da kasa, likita Amani sharif tana shirin fitar da wani littafi da ke dauke bayanin magunguna da suka zoa cikin kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadal balad cewa, likita Amani sharif malama ce a bangaren ilimin microbiology and eminology a jami'ar birnin Alkahira.

A wata zantawarta da wata kafar yada labarai ta bayyana cewa, hakika akwai abubuwa da dama da suka zoa a cikin kur'ani da suke Magana kan magunguna wadanda suka shafi tsirrai da hakukuwa wadanda suke da matukar amfani ta fuskar magani da dan adam.

Ta ci gaba da cewa yanzu haka ta kammala abubuwa da dama da suka shafi binciken da ta gudanar, wanda ta tabbatar da shi ta hanyar gwaje-gwaje da naurori na zamani, wanda da yardarm Allah za ta fitar da shi domin amfanar jama'a.

Likitan ta ce ko shakka babu magunguna na tsirrai suna dauke sanadarai na kariya ga jikin dan adam masu karfin gaske, kuma akwai abubuwan da mutane suke ganinsu ammaba su san amfaninsu, a kan ha kata yi iyakacin kokarinta domin iya fitar da abin da ta iya ganowa.

Kasar Masar dai ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar bincike a kan magungunan gargajiya da suka hada da tsirrai da sauransu, wanda hakan yak an taimaka matuka wajen yin mgani ga cututtuka da dama da ba a iya samun maganin bature a kansu ba.

3558930


captcha