Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya
habarta cewa, Jaridar Daily Nation ta kasar Kenya ta bayar da rahoton cewa,
shugaban kasar ta Kenya Uhuro Kenyatta ya bayyana cewa, yana da zimmar aiwatar
da wani sabon shiri na bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar ta hanyar
gudanar da ayyukan hadin gwiwa tare da bankin muslunci.
Kenyatta ya ce ko shakka babu za a amfana matuka a kasar Kenya da tsarin ayyukan bankin musulunci, domin kuwa akwai abubuwa da dama wadanda suka shafi harkokin zuba hannayen jari da ayyuka wadanda za su amfani kasar Kenya ta hanyar wannan baki.
Ya kara da cewa, yanzu haka magana ta yi nisa a tsakaninsu da manyan cibiyoyi a kasar Malaysia da suke da manyan hannayen jari a bankin muslucni, dangane da yadda za su yi aiki tare da kasar Kenya, wanda kuma a cewarsa, hakan zai bude kofa ga sauran kasashen Afirka su ci moriyar ayyukan bankin muslunci, domin kuwa a cewar Uhuru Kenyatta akwai abubuwa da dama da aka yi musu mummunar fahimta dangane da wanann banki, amma masana harkokin tattalin arziki sun yi imanin cewa suna da amfani, akan haka Kenya za ta zama a sahun gaba wajen yin mu'amala da wannan banki.