IQNA

Jagoran Juyin Islama:
23:50 - January 05, 2017
Lambar Labari: 3481103
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin Islama ya bayyana dakaru masu kare wurare masu tsarki na muslunci a matsayin abin alfahari ga al’ummar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a lokacin da yake ganawa da iyalan wasu daga cikin dakarun da suka yi shahada a lokacin da suke kare wurare masu tsarki na al’ummar musulmi, jagora ya bayyana cewa wadannan shahidai sun daukaka matsayin al’umma.

Dukkanin shahidan wadanda iyalansu suka gana da jagora, sun shahada ne wajen kare hubbaren Sayyidah Zainab (SA) a kasar Syria.

Jagoran ya kara da cewa, wasu daga matan shahidan sun yi wasu kalamai a lokacin bizne mazajensu, kalaman da suke dauke da ma’anoni na hakika dangane da shahada a tafarkin ubangiji.

Haka nan kuma jagoran ya yi ishara da cewa, da Iran ba ta sha gaban ‘yan ta’adda a Syria a ba, to da a cikin lardunan Tehran, Farsa, Khorasan da Isfahan ne za ta yi yaki da su.

3559982

http://iqna.ir/fa/news/3559982

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: