IQNA

Mahukuntan Kasar Bahrain Sun Sake Dage Shari’ar Sheikh Isa Kasim

23:54 - January 05, 2017
Lambar Labari: 3481104
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Bahrain sun sake dage shari’ar babban malamin addini na kasar Sheikh Ayatollah Isa Kasim zuwa karshen wannan wata.

Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gzio na shafaqna cewa, kotun masarautar Bahrain ta gudanar da zaman shari’ar da ta ce tana yi kan Sheikh Isa Kasim, tare da sanar da cewa ta sake dage zaman suwa karshen wannan wata na Janairu.

Tun a ranar hudu ga watan Disanban da ya gabata ne dai kotun ta bukaci bankin mustaqbal na kasar da ya kawo mata dkkanin bayanai da suka shafi sheikh Isa Kasim, dangane da asusunsa na ajiyar kudade, da kuma bayani kan dukkanin kudaden da suka shiga ciki daga lokacin bude asusun ya zuwa yanzu.

Masarautar Bahrain ta sanar da janye izinin zama dan kasa daga kan babban malamin addini na kasar Sheikh Ayatollah Isa Kasim, bisa hujjar cewa yana goyon bayan ‘yan adawar siyasa na kasar, tare da bayyana cewa yana karbar kudaden zakka da khumusi da mabiyansa ba shi, ba tare da izinin masarautar kasar ba.

3559967

http://iqna.ir/fa/news/3559967

captcha