IQNA

21:19 - January 10, 2017
Lambar Labari: 3481120
Bangaren siyasa, Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya jagoranci sallar janazar da aka gudanar a kan gawar marigayi Ayatollah hashimi Rafsanjani.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Ayatollah sayyid Ali Khamenei ne da kansa ya ja sallar mamacin a babban masallacin jami’ar birnin Tehran a safiyar yau tare da halartar dubban daruruwan al’umma na ciki da wajen kasar.

kafin hakan dai an shiga zamanmakoki na kwanaki uku domin juyayinrasuwar tsohon shugaban kasarwanda shi ne shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin muslunci ta Iran.

Da yammacin Ranar Lahadi ne Allah ya yi wa Ayatollah Rafsanjani rasuwasakamakon matsalar zuciya.

A rayuwarsa Ayatollah Rafsanjani ya rike mukamai da dama daga ciki kuwa har da shugabancin kasar ta Iran daga shekarar.

Za a ci gaba da amsar gaisuwa da ta’aziyya a Husainiyar Iamm Khomenei (RA) tare da halartar jagora, daga gobe Laraba 11/1/2016, daga misalign karfe 9:30 har zuwa 12:00.

3561451Jagoran Juyin Islama Ya Jagoranci Janazar Ayatollah Hashimi Rafsanjani

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: