Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, an fara gudanar da zaman ne a yau, tare da halartar Abu Zar Ibrahimi Turkamani, shugaban cibiyar yada al'adun muslunci ta Iran, Haddad Adel shugaban cibiyar al'adu da harshen farisanci ta kasa, Sayyid AbulHassan Nuwwab, shugaban jami'ar addinai, Muhammad mahdi Tehranchi shugaban jami'ar Shahid Beheshti kuma babban sakataren taron bunkasa al'adu tsakanin Iran da larabawa, wanda ake gudanarwa a cibiyar Zahra (SA) a birnin Tehran.
Zaman dai yana samun halartar masata 85 daga kasashen larabawa daban-daban, da suka hada da Algeria, Tunisia, Masar, Morocco, Syria, Lebanon, Iraki, Jordan, Kuwait, Oman da sauransu.
Babban abin da zaman taron ke yin dubi a kansa shi ne, hanyoyin da za a bi domin kara bunkasa al'adu na muslunci a tsakanin Iran da sauran kasashen larabawa, kasantuwar cewa dukaknin al'ummomin biyu suna tsohon tarihi wajen yin tarayya a cikin al'adu, kamar yadda kuma daga bisani addinin muslunci ya hada su a kan turba guda ta imani.
Baya ga haka kuma batun wayar da kan al'ummomi dangane da bin sahihin tunani madaidaici a cikin addini, tare da girmama fahimtar juna a dukkanin bangarori na addini ne ko na al'adu ko zamantakewa ko siyasa da dai sauransu.
Sayyid Rida Salihi Amiri ministan al'adu na kasar Iran, da kuma Muhammad kafi shugaban jami'ar Firdausi, dukkaninsu za su halarci zaman karshe na wannan taro a ranar Litinin mai zuwa.