IQNA

Rashin Tabbas Kan Makomar Lamurra A Matsayi Na Kasa Da Kasa

23:54 - January 23, 2017
Lambar Labari: 3481163
Bangaren kasa da kasa, Netanyahu na cikin taka tsantsan danagne da tofa albarkacin bakinsa kan abubuwan da ka iya zuwa su dawo dangane da sabuwar siyasar Amurka.

BKamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNa ya habarta cewa, Netanyahu Firayi ministan Isra'ila na daga cikin wadanda suke bin lamurra ahankali kan makomar siyasar kasar Amurka dangane da Isra'ila bayan da Trump ya lashe zabe.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa jim kadan bayan rantsar da shi, Trump ya bayyana cewa Amurka da Amurkawa su ne farko a wajensa kafin kowa da komai, kamar yadda kuma ya yi ishara da cewa zai fi mayar da hankali wajen ayyukan cikin gida ne fiye da ayyukan a wajen kasar da Amurka take gudanarwa.

Hakika Amurka ta saka kafa a cikin sabbin kalu bale daga shekara ta 2017 bayan da Donald Trump ya karbi shugabancin kasar daga ranar ashirin ga wannan wata na Janairu, kuma dukkanin wadannan kalubale suna da alaka da shi Trump, ta fuskar siyasa ne ko tattalin arziki ko zamantakewar al’ummar kasar wadda ta hada mabanbantan al’adu da al’ummomi da ma addinai, da kuma ta fuskar tattalin arziki, bugu da kari kan hakan siyasar wajen kasar da kuma sauran batutuwa da suka shafi alakarta da kawayenta na turai, da kuma wadanda take takun saka da su.

An sha jin Donald Trump yana sukar karbar baki ‘yan gudun hijira musaman ma musulmi daga cikinsu, amma kalamansa sun canja dangane da hakan bayan da ya lashe zabe, kamar yadda kuma yake caccakar kasar Saudiyya tare da bayyanata a matsayin kasar da ke yada tsatsauran ra’ayi da ta’addanci, duk kuwa da cewa da wuya wani abu ya iya raba alakar da ke tsakanin Saudiyya da Amurka, bisa la’akari da matsayin kasar ta Saudiyya a cikin kasashen larabawa da kuma na musulmi, inda Amurka kan yi amfani da ita cikin sauki wajen cimma manufinta a kan kasshen larabawa da na musulmi.

Dangane da batun Syria kuwa, Trump ya bayyana Bashar Assad a matsayin asharari, amma kuma duk da haka ya ce ba zai yake shi ba, yaki da ‘yan ta’adda shi ne mafi muhimmanci a gare shi.

Amma dangane da Iran kuwa Trump bai taba boye tsananin adawarsa da ita ba, inda har ma yake yin barazanar yin watsi da yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa a tsakaninta da manyan kasashen duniya. Kamar yadda kuma ya jaddada goyon bayansa ga Isra’ila da siyasarta a yankin gabas ta tsakiya, duk kuwa da cewa dora wasu daga cikin fitattun Amurka masu tsananin ra’ayin ‘yan kasanci a kan muhimamn mukamai na kasar, ya sanya Isra’ila tana yin taka tsantsan matuka dangane da saurin furta kalamai da suka shafi Trump da kuma abubuwan da yake shirin aiwatarwa, duk kuwa da alkawalin da ya yi na dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa Quds.

Dangane da alakar Amurka da Rasha wadda ta tabarbare a lokacin Barack Obama, amma lokacin yaki neman zabe Donald Trump ya yi ishara da cewa zai yi kokarin ganin ya daidaita alaka da Rasha, kamar yadda kuma ya soki kungiyar tsaro ta nato kan ayyukanta, musamman ma jibge makamai a gabashin turai domin fuskantar abin da suke kira barazanar tsaro daga Rasha, inda har ma ya yi barazanar ficewar Amurka daga cikin kungiyar ko kuma rage ayyukanta, lamarin da ya daga hankulan kasashen yammacin turai matuka.

To sai dai abin da yake tabbatace a siyasar Amurka ba abu ne mai sauki ga Donald Trump ya iya canja shi ba, domin kuwa a kowane lokaci siyasar Amurka ta ginu ne kawai a kan maslaha ba gaskiya ko yin abin da ya dace ba, wanda hakan yasa masana harkokin siyasar kasa da kasa da dama suke ganin cewa, Donald Trump da aka sani a lokacin da yake yakin neman zabe da kuma Donald Trump da ya shiga fadar White House a yanzu, za su zama suna da bambanci, duk kuwa da cewa har yanzu bai fara aiwatar da komai ba balantana a iya gane kamun ludayinsa.

3565336


captcha