IQNA

Mutane 21 sun Rasu A Wani Harin Bam A Wata Kasuwar Kayan Rani A Pakistan

23:56 - January 23, 2017
Lambar Labari: 3481164
Bangaren kasa da kasa, Akalla mutane 21 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani bam da aka kai a kan wata kasuwar sayar da kayan rani a garin Barashinar na mabiya mazhabar shi'a a kasar Pakistan.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na «Aljazeera» cewa, an kai harin da bama-bamai a lokacin da mutane suke hada-hadar saye da sayarwa a cikin kasuwar kayan ranin, kuma a nan take mutane 21 ne suka riga mu gidan gaskiya.

Kungiyar Taliban bangaren Hakimullah Mahsud ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce ta yi hakan ne domin daukar fansa kan kashe 'yan uwansu da ke yaki a Syria da Bashar Assad ke yi.

Rahotn ya ce an dauki mutane kimanin 40 suka samu munan raunuka zuwa asibitin soji da ke garin Bishawur domin yi musu maganai, 12 daga cikin wadanda suka samu raunuka suna cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

3564858
captcha