IQNA

Cibiyar Musulmin Amurka Ta Mayar Da Martani Kan Hana Musulmi Shiga Kasar

22:19 - January 25, 2017
Lambar Labari: 3481168
Bangaren kasa da kasa, cibiyar musulmin kasar Amurka ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da matakin da shugaban kasar ke shirin dauka na hana musulmi shiga kasar.

Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «PRNewswire» cewa, majalisar musulmin kasar Amurka ta gudanar da taro a yau inda ta yi Allawadai da shirin gwamnatin kasar na neman hana wasu musulmi daga wasu kasashe izinin shiga kasar.

Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump na shirin sa hannu kan dokar da za ta hana bayar da izinin shiga kasar ga mutanen Syria da kuma wasu kasha 6 na musulmi.

Trump yana da nufin hana mafi yawan yan gudun hijira shiga cikin kasar Amurka na wucin gadi, kamar yadda zai harmta bayar da izinin shiga ga mutanen kasashen Iran, Syria, Iraki, Libya, Somalia, Sudan da kuma Yemen.

Tun a lokacin yakin neman zabe ya bayyana cewa zai hana musulmi shiga kasar Amurka, saboda bayyana su da yake yi a matsayin yan ta'adda, wanda kuma abin da yake a yanzu yana a matsayin aiwatar da alkawullan nasa ne.

Majalisar muuslminkasar ta Amurka ta bayyana wanann mataki da cewa ya yi hannun riga da dukkanin abubuwan da aka girka kasar a kansu, kuma hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

3566636


captcha