IQNA

22:22 - January 25, 2017
Lambar Labari: 3481169
Bangaren kasa da kasa, wasu yan kungiyar Boko Haram sun yi nufin kaddamar da wasu hare-hare a cikin birnin Maiduguri na jahar Borno a yau, amma hakan bai yi nasara ba.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saharareporters cewa, hari na farko an shirya kai shi ne kan gidan wani mutum daga cikin 'yan banga masu gudanar da binciken abubuwan hawa.

A lokacin da 'yan ta'addan suka isa gidansa sun buga kofa amma yaki budewa, sai dai wata mace wadda take dauke da jigidar bama-baman ta rungumi wani mutum mai wucewa, wanda suka tarwatse tare.

Haka nan kuma wani dan ta'addan shi ma ya nufi wani masallaci da nufin kasha adadi mai yawa na msallata, amma bai samu damar yin hakan ba, domin kuwa jama'a sun gane shi, inda daga karshe dai bam din da ke jikinsa ya halaka shi har lahira.

Tun a cikin shekara ta 2009 ce dai 'yan ta'addan Boko haram suka fara kaddamar da hare-hare da bama-bamaia cikin Najeriya, inda suka kasha dubban mutane, tare da mayar da fiye da miliyan 2.6 yan gudun hijira.

Tarayyar Najeriya ta dauki kwararan matakai na shiga kafar wando daya da wadannan yan ta'adda amma dai hakan bai iya kawo karshensu ba, sai a cikin lokutan nan an ci karfinsu a dajin da suka kafa babbar tungarsu.

3566914


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: