IQNA

Ma'aikatar harkokin Wajen Iran Ta Kirayi Jakadan kasar Swissland

22:38 - January 29, 2017
Lambar Labari: 3481181
Bangaren kasa da kasa, Kakakin Ma'aikatar harkokin Wajen Iran ya sanar da kiran jakadan kasar swissland domin nuna masa kin amincewar Iran da matakin Shugaban Kasar Amurka na kin jikin 'yan gudun hijira.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, Kakakin Ma'aikatar harkokin Wajen Iran ya sanar da kiran jakadan kasar swissland domin nuna masa kin amincewar Iran da matakin Shugaban Kasar Amurka na kin jikin 'yan gudun hijira.

Bahram Kasimy yaci gaba da cewa; An gabatarwa da jakadan kasar ta Swissland takardar kin amincewa ne da dokar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi, na hana yan kasar Iran shiga kasar tare da bayyana hakan a matsayin nuna wariya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya ci gaba da cewa; Dalilin da Amurkan ta bijo da shi, ba shi da madogara, kuma yana cin karo da dokokin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu akan dokar hana yan kasashen bakwai na musulmi shiga cikin kasar ta Amurka, Kasashen sune Iran da Iraki da Sudan da Somaliya da Libya da Syria da Yemen.

3568127


captcha