IQNA

22:40 - January 29, 2017
Lambar Labari: 3481182
Bangaren kasa da kasa, mutane suna ta nuna rashin goyn bayan hana muuslmi daga kasha 7 shiga cikin kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «kdvr» cewa, daruruwan matafiya Amurkawa sun taru a cikin filaye safka da tashin jiragen sama suna ta rera taken nuna goyon baya ga musulmi da aka hana su shiga cikin kasar Amurka.

A lokacin da wasu daga cikin matafiya musulmi da aka hana su shiga cikin Amurka suke gudanar da salla, daruruwan Amurkawa sun zagaye suna rera taken a kyale musulmi su sallarsu, suna masu ba su kariya.

Wani ma'aikaci a cikin filin safkar jirgin sama a Doner a kasar Amurka ya sheda cewa, bai taba ganin jama'a suna gangami da nuna kyma ga wani mutum ba arayuwarsa kamar yadda ya gani a yanzu mutane suna nuna kyama ga Donald Trump da siyasarsa.

Bisa ga umarnin da Donald Trump ya bayar musulmi daga kasashe 7 wato Iran, Syria, Yemen, Iraki, Sudan, Somalia da kuma Libya, bas u da hakkin shiga Amurka daga nan zuwa kwanaki 90, kuma an dakatar da karbar 'yan gudun hijira har zuwa kwanaki 120 masu zuwa.

Wannan mataki na Trump dai yana ci gaba da shan kakausar suka daga koina cikin fadin duniya, yayin da zanga-zangar kin jininsa da la'antarsa ke ci gaba da kara bazuwa zuwa wasu sassa na kasar.

3568013


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: