IQNA

Kakkausar Sukar Magajin Garin New York A Kan Siyasar Donald Trump

16:52 - January 30, 2017
Lambar Labari: 3481185
Bangaren kasa da kasa, Magajin garin birnin New York na kasar Amurka ya yi kakkausar suka dangane da salon siyasar shugaban kasar Donald Trump ta nuna wariya da kyamar baki 'yan kasashen ketare.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, Jaridar Independent ta habarta cewa, magajin garin birnin New York Bill de Blasio ya bayyana siyasar Donald Trump da cewa ta yi hannun riga da dukkanin dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Ya ce ba su za su taba yin biyayya ga umarnin Donald Trump ba, domin kuwa ya sabawa dokar kasa, kuma zanga-zangar da ake yi domin nuna kyamar siyasar Trumpa birnin New York da sauran biranan kasar Amurka tana akn doka, kuma hakan somin tabi ne na kalubalantar siyasar wariya ta Donald Trump.

Haka nan kuma magajin garin na birnin New York ya bukaci jam'iyyun Republican da Democrat da sauran 'yan siyasa masu zaman kansu a kasar ad su fito su takawa Trump burki, tun kafin ya rusa kasar Amurka.

3568184


captcha